Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na na Ahlul Baiti (AS) – ABNA– ya habarto cewa: Muhammad Al-Bakhiti, mamba a ofishin siyasa na Ansarullah, ya yi jawabi ga Hamas da Jihadin Islama: Ba za mu tsoma baki cikin cikakkun bayanan tattaunawar ba saboda yanke qudiri na ku ne, amma muna biyayya ga alkawarin da muka yi muku; aikin sojan da aka kaddamar bisa bukatar ku, za mu dakatar da shi ne kawai bisa bukatar ku’ kuma za a ci gaba da kaiwa a duk lokacin da kuke so. Makomarku ita ce makomarmu, muna tare da ku har zuwa nasara ko shahada.

Kungiyar Hamas ta bayar da wani martani mai cike da sharadi kan shirin Donald Trump mai dauke da batutuwa 20, inda ta sanar da cewa a shirye take ta sako mutanen da aka yi garkuwa da su da kuma shiga tattaunawa. A sa'i daya kuma, Trump ya yi kira ga Isra'ila da ta gaggauta dakatar da kai harin bam a Gaza.
Your Comment